China da Indiya na yunkurin kyautata dangantakarsu
September 18, 2014Shugabannin kasashen China da Indiya sun yi alkawarin kawo karshen rikicin kan iyakar da ya addabi kasashensu. Bayan wata ganawa tsakanin shi da Xi Jinping na China a birnin New Delhi na kasar Indiya, Firaministan Indiya Narendra Modi ya bayyana cewa, idan har babu kwanciyar hankali a kan iyakar kasahe makota, zai yi wahala a yi wani kawance na arziki.
A na sa bangaren Xi Jinping na Chinan ya ce kasarsa ta yanke shawarar shawo kan matsalar ta hanyar tattaunawa, kuma a halin da ake ciki, ya zama wajibi kasashen biyu su janye dakarunsu daga yankin Ladakh inda rikicin ya fi kamari domin kawo sassauci.
Da wannan ziyara ta Xi Jinping na China, shugaban na fatan kara kyautata dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu wadanda su ne suka fi karfin tattalin arziki a yankin Asiya. Dan haka ne ma ya ce gwamnati a Beijing za ta zuba jarin milliyan dubu 20 a Indiya nan da shekaru biyar masu zuwa.