China: Bude taron jam'iyyar kwamunisanci
October 18, 2017Talla
Jam'iyyar kwamunisanci ta China a yau Laraba ta fara babban taronta na kasa karo na 19.
A jawabinsa shugaban kasar Xi Jinping ya jinjinawa nasarorin da kasar ta samu a cikin shekaru biyar da suka wuce.
Ya bukaci 'yan jam'iyyar su kaucewa dukkan wani abu da zai tauye martabar kasar da kuma akidun da ta tsaya akan su.
Taron jam'iyyar wadda akan gudanar duk bayan shekaru biyar zai zabi sabbin shugabanni inda kuma ake sa ran Xi Jinpin zai sami wa'adin mulki karo na biyu na shekaru biyar a matsyin shugaba.
Wakilai fiye da 2000 ne ke halartar taron.