Babban taron jam'iyyar Kwaminis yayin raunin tattalin arziki
March 5, 2019Kasar China wadda ke a jerin kasashen duniya masu karfin tattalin arziki yanzu haka tana fama da tarin basussuka da a kullum yawansu ke karuwa. Ana dai cikin wani halin rashin tabbas a daidai lokacin da babbar jam'iyyar da ke mulki ta Kwaminisanci ta fara babban taronta na shekara-shekara a birnin Beijing.
Sai dai a wata sabuwar manhaja ta farfaganda da mahukunta kasar suka kirkiro na da nufin cusa ra'ayin shugaban kasa Xi Jinping kuma shugaban jam'iyyar da ke mulkin kasar a kawunan 'yan China, tare da yada akidarsa mai taken "Sabon Zamani na Gurguzu". Sai dai masu sukar lamirin hukumomin na cewa duk wanda ya nuna irin wannan bukatar ta farfaganda ba shakka yana fuskantar barazana. Yanzu haka dai manhajar ita ce kan gaba a jerin manhajojin da aka fi amfani da su a kasar China watakila saboda amfani da ita dole a tsakanin da yawa na ma'aikatan gwamnati.
Babban taron jam'iyyar Kwaminisanci zai duba batun saka hannun jari
Ana cikin dar-dar a daidai lokacin da aka fara babban taron shekara-shekara na jam'iyyar Kwaminisanci, inda a baya bayan nan sai da Shugaba Xi Jinping ya kira wani taron gaggawa na daruruwan sojoji a kan kalubalen da China ke fuskanta ciki har da takaddamar kasuwanci da Amirka da bashin da ke kan kasar da barazanar durkushewar kamfanoni sai kuma yiwuwar karuwar yawan marasa aikin yi a kasar. Duk da haka a cewar mai sukar lamiri, farin jinin shugaba Xi na raguwa.
A babban taron jam'iyyar a bara, ya canja dokokin tsarin mulki da ya janye takaita wa shugaban kasa wa'adin mulki. To amma sai dai a bana dokar ka'idojin zuba hannun jari daga ketare ne ke kan gaba a taroni, abin da ke zama wata alamar cewa mahukuntan na China za su dauki karin matakai na bude kofofin kasuwannin kasar kamar yadda ake nuna bukata. Wang Yang shi ne shugaban kwamitin mashawartan majalisa ya ce kasar China na cikin wani sabon zamani na tarihi, saboda hakan dole ne mu bayar da goyon baya ga kwamitin jam'iyyar Kwaminisanci karkashin shugabanmu Xi Jinping da ke fafutikar karfafa akidar gurguzu a China.