Chamisa: Zan kalubalanci zaben Zimbabuwe
August 2, 2018Manyan 'yan takara a zaben shugaban Kasar Zimbabwe na ci gaba da ikirarin samun nasara a zaben da ya gudanar ranar Litinin, a daidai lokacin da ake ci-gaba da dakon cikakken sakamakon daga hukumar zabe mai zaman kanta. Masu sa ido na kasa da kasa sun bukaci hukumar zaben da ta hanzarta sanar da sakamakon don kauce wa tashin hankali bayan kashe mutane shida a ranar Laraba a wani rikici tsakanin jami'an tsaro da magoya bayan 'yan adawa.
Madugun 'yan adawa Nelson Chamisa ya bayyana cewa shugaba mai ci a yanzu Emmerson Mnangagwa ya rigaya ya san ya fadi zabe, saboda haka zai kalubalanci sakamakon zabe idan aka samu akasi. Amma kuma jam'iyyar ZANU-PF da ke mulki ta ce dan takararta na kan samun nasara.
Sojoji sun killace manyan titunan birnin Harare duk da kira da kasashen waje da kungiyoyin duniya suka yi na a kwantar da hankali don da ka da a jefa kasar cikin rikicin siyasa.