Chaina ta yi gwajin makami mai lizzami
May 9, 2017Kasar Chaina ta sanar da yin gwajin wani sabon na'in makami mai lizzami a tekun Bohai ta kusa da Koriya ta Kudu. Wannan gwaji ya zo ne a daidai loakcin da ake cikin zaman doya da man ja tsakanin Chainar da Koriya ta Kudun wacce ta gudanar da zaben shugaban kasa a wannan Talata.
A cikin wata sanarwa data fitar, ma'aikatar tsaron kasar ta Chaina ta ce gwajin makamin nata na da burin bunkasa karfin wuta na sojin kasar, ta yadda za su fi iya fuskantar duk wasu kalubalai na tsaro da za su tunkaro kasar.
A makon da ya gabata dai kasar Chaina ta gargadi Amirka da ta dakatar da shirinta na girke na'urorin tarar makamai masu linzami na Thaad da ta soma a Koriya ta kudu da nufin taka birki ga shirin nukiliyar koriya ta Arewa, shirin da Chainar ta ce na a matsayin wata babbar barazana ga harkokinta na tsaro.