Chadi: Gangamin adawa da tazarcen Deby
March 10, 2016Shugaba Idriss Deby Itno na neman tsawaita mulkinsa na shekaru 26, a zaben da zai gudana a wata mai zuwa.
Neman tazarce a karo na biyar na shugaban kasar ta chadi dai na fuskantar adawar da ta hada da zaman dirshan da al'ummar kasar ta yi a a watan da ya gaba, batu da ya jagoranci tsayar da harkokin karatu da ma kasuwanci a dukkan fadin kasar.
A wani mataki na baya bayannan, kungiyoyin farar hula 12 ne suka yi kira ga al'ummar Chadin da su hura wusil na mintuna 15 da sanyin safiya da kuma daren yau Alhamis, domin nuna bukatar cewar tura ta kai bango dangane da cin zarafi da rashin adalci da cin hanci da nuna son daura da wahalhalu na rayuwa da jama'a ke fuskanta a ko wace rana.
Duk da sabbin rijiyoyin mai da aka gano a kasar dai, Chadin na ci gaba da kasancewa cikin talauci, a daidai lokacin da ake zargin Deby da hannu a cafke masu adaw da shi. A shekara ta 2004 ne dai ya goge sashin kundin tsarin mulkin kasar da ke ba wa ko wane shugaba wa'adin mulki sau biyu, batu da ya bashi damar lashe zabukan 2006 da 2011.