Chadi: Fafutikar sakin Tadjeddine Mahamat
January 18, 2018Tun dai a ranar 13 ga wannan wata na Janairu aka kafa kwamiti a wani mataki na fadada bukatar neman a sallamo dan fafutikar daga tsaron da ake yi masa tun daga tsakiyar watan Satumba na 2016 sakamakon wasu kalamai da ya yi na suka ta shafinsa na Facebook ga shugaban kasar ta Chadi Idriss Deby Itno. A cewar mai magana da yawun kwamitin da aka kafa Jean-Bosco Manga yanzu dai sun shigar da kara domin ganin an sake shi
A cewar kungiyar kare hakin bil-Adama ta Amnesty International, an dauke dan fafutikar Tadjeddine Mahamat Babouri yayin da yake tafiya a tsakiyar titin birnin N'Djamena 'yan kwanaki kalilan bayan da ya wallafa wani bidio na sukar Shugaba Deby, inda ake ci gaba da tsare shi a gidan kaso na Moussoro da ke tsakiyar kasar bayan da ya shafe watanni da dama a gidan kaso na Koro Toro da ke arewacin kasar.