1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadi: Dakile juyin mulki ko bita-da-kulli?

Mouhamadou Awal Balarabe
January 6, 2023

Hukumomin Chadi sun kama sojoji 11 da shugaban hukumar kare hakkin bil'Adama na kasar, bisa zargin yunkurin tada zaune tsaye da nufin kawo cikas ga tsarin tafiyar da kasar. Kotu ta fara bincike don gano gaskiyar lamarin.

https://p.dw.com/p/4LpYh
Shugaban gwamnatin mulkin soja na Chadi Mahamat Idriss Deby ItnoHoto: Denis Sassou Gueipeur/AFP

Hukumomin Chadi sun shafe makonni hudu suna rufa-rufa kan batun da suka danganta da yunkurin juyin mulki, kafin su fitar da sanarwa a ranar Alhamis da maraice da ke nuna cewar sun dakile shi. Sun danganta Baradine Berdei Targuio da ke zama shugaban hukumar kare hakkin dan Adam ta Chadi da zama kanwa uwar gami na yunkurin tada zaune tsaye da nufin kawo cikas ga mulki da kuma hukumomin kasar. Sannan mahukunta na Ndjamena suna zargin sojoji 11 da marar hannu a abin da suka kira manakisa, lamarin da ya sa suka kama su tun ranar 8 ga watan Disemban 2022.

Gwamnati ta ce za ta yi cikakken bayani

Ministan yada labarai kuma kakakin gwamnatin Chadi Aziz Mahamat Saleh ya nunar da cewa kotu ta kaddamar da binciken bisa zargin zagon kasa ga tsarin mulkin kasa da mallakar makamai ba bisa ka'ida ba da kuma hada baki don cutar da kasa. Hasali ma dai, sanarwar da aka raba wa manema labarai ta bayyana cewa alkali ya riga ya tuhume su tare da tura su gidan yari.

Tschad | Eröffnung Nationaler Dialog in N'Djamena
Mahamat Deby da mukarrabansa za su yi karin haske kan yunkurin juyin mulkiHoto: Aurelie Bazzara-Kibangula/AFP/Getty Images

Gwamnatin Chadi ta yi alkawarin yin cikakken bayani nan gaba a kan wannan lamarin. Sai dai Evariste Ngarlem Toldédon da ke nazari kan lamaran siyasa a kasar, ya ce akwai lauje cikin nadi. Ya ce: " Akwai wani rashin kwanciyar hankali da ke tattare da bangaren da ke mulki a halin yanzu, domin baya ga wannan sanarwar yunkurin juyin mulki da aka fitar, an tsige kanin marigayi Idriss Deby Itno daga mukaminsa a hakumar 'yan sanda bisa wannan dalili."

Gwamnatin mulkin sojan Chadi ta jima tana takun saka da Baradine Berdei Targuio da ake zargi da yunkurin kitsa juyin mulki. Tun bayan fara fafutukar kare hakkin bil'Adama a kasar Chadi, Berdei Targuio ya kasance a sahun gaba wajen sukar shugaban kasa da salon mulkinsa a shafukan sada zumunta. ko a  watan Fabrairun 2021, sai da aka yanke masa hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari saboda rubutawa da ya yi cewa shugaban kasa na wancan lokaci, Idriss Deby Itno na fama da rashin lafiya mai tsanani.

Ana yi wa Berdei Taguio Bita-da-Kulli?

Tschad Mahamat Idriss Déby Itno
Mahamat Déby Itno ya saba takura wa masu adawa da mulkinsaHoto: Marco Longari/AFP/Getty Images

Sai dai a wannan karon, matsayinsa na wanda ya mallaki bayanai game da halaka tsohon shugaban kasa Idriss Deby Itno ya shafa masa kashin kaji, a cewar Evariste Ngarlem Toldédon da ke nazari kan lamaran siyasa a Chadi. Ya ce: " Ku tuna cewa shekaru biyu zuwa ukun da suka gabata, gwamnati ta yi zawarcin Baradine Berdei Targuio don ya bada gudunmawa, amma ya ce akai kasuwa. Ga shi a yau ana tuhumarsa da laifin mallakar makamai ba bisa ka'ida ba, lamarin da ya musanta. Ana neman hanyar hana shi tona asiri kan musabbabin mutuwar marigayi Deby Itno. Wannan ne ya sa ake yi masa bita-da-kulli."

Juyin mulki ya zama ruwan dare a Chadi

Tun a ranar 20 ga Afrilun 2021 ne Janar Mahamat Deby ya hau kan karagar mulki bayan mutuwar mahaifinsa da  'yan tawaye suka kashe a fagen yaki, bayan ya yi mulkin kama karya a kasar Chadi na tsawon shekaru 30. Amma bayan da ya rusa majalisar dokoki da dakatar da kundin tsarin mulkin Chadi, sabon shugaban mulkin na soja ya yi alkawarin mayar da mulki a hannun farar hula bayan gudanar da zabe cikin 'yanci da walwala.

Sai dai tun bayan samun ‘yancin kai daga Turawan Faransa a shekarar 1960, tarihin kasar Chadi ne cike da juyin mulki da hare-haren ‘yan tawaye.