1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadi: Mahamat Idriss ya zama shugaban riko

Abdoulrazak Garba Babani MNA/RGB
April 20, 2021

An nada Mahamat Idriss a matsayin shugaban riko a kasar Chadi bayan mutuwar mahaifinsa Idriss Déby Itno a wannan Talata. Rundunar sojin kasar ce ta sanar da mutuwar shugaban.

https://p.dw.com/p/3sFJG
Tschad Mahamat Idriss Déby Itno
Shugaban riko Mahamat Idriss Déby ItnoHoto: Marco Longari/AFP/Getty Images

Rundunar sojin Chadi ta sanar da nadin Janar Mahamat Idriss dan marigayi Idriss Deby a matsayin shugaban riko na kasar. Janar Mahamat zai rike gwamnatin Chadi ne na watanni 18 kafin kafa wata sabuwar gwamnati. Shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya rasu ne a wannan Talata 'yan sa'o'i bayan da aka bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a baya-bayan nan. Rundunar sojin kasar ta Chadi ce ta sanar da mutuwar shugaban, inda ake zullimin ya mutu ne a sanadiyyar raunin da ya samu a fagen daga, wurin yaki da 'yan tawayen da ke hankoron kwace ikon gwamnatin kasar. Mutuwar shugaban mai shekaru 68 a duniya na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke fuskantar barazanar fadawa cikin yakin basasa. Daga bisani, sojojin sun nada Mahamat Idriss Déby Itno daya daga cikin yaran marigayin a matsayin shugaban kasar na riko, Mahamat dan shekaru talatin da bakwai da haihuwa, janar ne a soja kuma shi ne ke jagorantar rundanar dogaran da ke tsaron fadar shugaban kasa.

Tschad Präsident Idriss Deby Itno
Deby ya mutu yana da shekaru 68Hoto: DW/B. Dariustone

Da safiyar wannan Talata, hukumar zaben kasar ta sanar da sakamakon zaben shugaban kasar da ta ce Shugaba Deby ne ya lashe da gagarumin rinjaye, jim kadan da sanarwar sojoji suka sanar da mutuwar Shugaba Idriss Deby Itno. Nasarar da bai mutu ba, za ta ba shi damar ci gaba da mulkin kasar a karo na shida. Sakamakon zaben na ranar 11 ga watan Afirilun da muke ciki, na zuwa bayan wani atisayen da dakarun sojin kasar suka yi a manyan titunan babban birnin kasar na N'Djamena. A na shi bangaren ma dai, madugun 'yan tawayen kasar, Mahamat Mahadi Ali ya zargi Faransa da daure wa shugaba Deby gindi da ma zama kanwa uwar gami a Chadin, amma yanzu duk wannan ya zama tarihi a yayin da ake jiran yadda lamuran kasar za su kasance bayan rashin shugaban da ya sha fafutuka don ganin kasar ta zauna lafiya daga hare-haren 'yan bindiga. Karin Bayani:  Mafita ga yankin Sahel da Tafkin Chadi

A ranar Litinin din da ta gabata, rundunar sojin kasar Chadi ta sanar da cewa, sojojinta sun yi nasarar hallaka 'yan tawaye kimanin 300 da suka kutsa arewacin kasar da zummar kwace mulkin sama da shekaru 30 daga hannun Shugaba Idris Deby .'Yan tawayen dai da suka bar kasar Libiya a ranar 11 ga watan nan na Afrilu, sun kutsa har zuwa wani yanki mai tazarar kilomita 300 daga N'djamena babban birnin kasar. Tun da misalin karfe 10 na safiyar ranar Litinin din, jama'a a birnin N'djamena suka shiga rudu, sun rikice kowa sai gudu yake ba tare da sanin dalilin ba. Sai dai an yi hasashen cewa a daidai wannan lokaci ne sojojin gwamnatin Chadi suka ajiye tankunan yaki a muhimman wurare irin su shataletale da ake da su a Ndjamena. Ko ma a baya 'yan tawaye sun ce a cikin kwanaki uku za su shiga birnin na N'djamena.

Zentralafrikanische Republik Ausschreitungen Gewalt Christen Muslime 16.01.14
Rikicin 'yan tawaye ya jefa Chadi cikin rudaniHoto: Eric Feferberg/AFP/Getty Images

Karin bayani: Harin bam ya halaka sojojin Chadi a Mali

Wannan al'amari a halin yanzu ya rikitar da garin, inda kusan kashi 85 cikin 100 na shaguna da kasuwannin tsakiyar birnin sun rufe jama'a da 'yan makarantu kowa ya koma gida, gari kuma ya yi tsit. Rundunar sojin Chadi ta ce ta kuma kame 'yan tawaye 150 tare da jikkata da dama. Ita kuma a bangarenta Chadi ta rasa sojoji biyar, wasu 36 sun jikkata. Tuni aka aiyana zaman makokin shugaban da ya kwashi fiye da shekaru talatin yana mulkin kasar.