Chadi: An kama masu sukar gwamnati
November 18, 2016A ranar Alhamis din da ta gabata ce dai hukumomin na Chadi suka kama masu nuna rashin amincewarsu da kamun ludayinta musamman wajen yin ayyukan da talakawa za su amfana da su. Gabanin kame mutanen dai wanda galibinsu 'yan adawa ne, jami'an tsaro sun tarwatsa wani gangami da suka shirya yi a Ndjemena babban birnin kasar. Kimanin mutane 30 ne dai aka kama a samamen da jami'an tsaro suka kai ciki kuwa har da Muhammad Bashir Bahar wanda ya yi fice wajen sukar manufofin shugaban kasar Idriss Deby Itno.
Wannan kamen da aka yi dai na zuwa ne kwana guda bayan da gwamnati ta sanar da haramcin da ta sanya kan dukkannin wani gangami ko zanga-zanga ko da kuwa ta lumana ce a fadin kasar, lamarin da 'yan adawa da kungiyoyin fararen hula da kuma 'yan rajin kare hakkin dan Adam suka yi Allah wadai da shi, inda suke cewa hakan ya sabawa 'yanci na fadin albarkacin baki.
A daura da wannan kuma, 'yan majalisar dokokin kasar sun yi yunkuri na kada kuri'ar yanke kauna da gwamnatin kasar ta Chadi da wadda firaministan kasar ke jagoranta, sai dai wannan lamari bai samu nasara ba kasancewar shugaban majalisar ya dage zamanta kana 'yan majalisar da ke jam'iyya guda da shugaban kasar da ma wanda ke kawance da ita sun kauracewa zaman majalisar.