Mummuna martani daga Ruwanda
June 26, 2015Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta bude sharhi akan wannan batu ne da taken " Capke dan Ruwanda a London ya samu mummun martani" ta ci gaba da cewar a ranar Asabar da ta gaba ne 'yan sanda suka capke janar Emmanuel Karenzi Karake a filin sauka da tashin jiragen sama na Heathrow da ke laondon, bisa ga warantin kame na Tarayyar Turai, duk da cewar sai ranar Talata aka sanar da kamun na sa. Mai shekaru 54 da haihuwa babban jami'in leken asirin na kasar Ruwanda na kan hanyarsa ce ta komawa gida bayan wani balaguro.
Kamar yadda ake zato dai gwamnatin Ruwandan ta nuna bacin ranta dangane da wannan kame wanda ta ce yana da alaka da siyasa. Ministan harkokin wajen kasar Louise Mushikiwabo ya ce ba zasu taba amincewa da wannan ba. Tun ashekara ta 2008 ne dai wani Alkalin kotun kasar Spain ya bada waranti kama manyan jami'an gwamnatin Ruwanda guda 40 ciki har da janar Karake, akan zargin da ake musu da tabka laifufukan ta'addanci lokacin kisan kiyashi na shekara ta 1994. Zargin ya hadar da kashe wasu jami'an agajin kasar Spain a Ruwanda, da kuma kisan ramuwar gayya akan 'yan kabilar Hutu 'yan dake gudun hijira a Kinshasa- Kongo, a shekarun 1997-98.
Ita ma a tsokacinta dangane da wannan batu a wani sharhi da ta rubuta mai taken.."Gawurtacen Janaral na Rwanda na garkame a Britaniya" jaridar Die Tageszeitung ta ce capke babban jami'in leken asirin na Ruwanda a ranar Asabar, abu ne da ke da muhimmanci shekaru 7 bayan gabatar da wantain kamashi da wasu mukarrabansa guda 40 da wata babbar kotu ta yi a Spain. Tuni dai aka gurfanar da Janar Karake a gaban kotun Majistrate na Wesminster da ke birnin London, inda daga nan za'a shirya yadda za'a mika shi ga hukumomin Spain.
Zaben 'yan majalisa mai sarkakiya a Burundi
Jaridar Die Tageszeitung kazalika ta yi sharhi dangane da zaben kasar Burundi mai sarkakiya da ake shirin gudanarwa a wannan Litinin mai zuwa. Tuni dai rigingimu ke kara yin kamari gabannin zaben 'yan majalisar dokokin da kawo yanzu ba'a san yadda zai kasance ba. Ana ci gaba da fuskantar fashewar gurneti, ayayin da 'yan adawa ke cigaba da tderewa daga kasar domin neman mafaka a ketare.
A wannan Talatar ce dai mataimakin shugaban kasar Gervais Rufyikiri dake gudun hijira a kasar Belgium ya bayyana a gidan atalabijin yana mai cewar ba zai ci gaba da goyon bayan abubuwan da gwamnatin shugaba Piere Nkurinziza ke yi wanda ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar ba. A wannan larabar ce kuma aka sanar da yiwuwar tserewar kakakin majalisar Burundinn Pie Ntavyohanyuma zuwa Brussels domin fakewa daga rikicin siyasar kasar.
Nkurunziza da ke shugabantar tsohuwar kungiyar mayakan sakai na kabilar Hutu dai na neman sake yin takara na wasu shekaru biyar a karo na uku, duk da cewar ya sabawa kundin tsarin mulki wanda ke bada wa'adi biyu ga ko wane shugaba. Gangamin adawa da wannan yunkuri nasa ya zuwa yanzu ya yi sanadiyyar rayukan mutane 70, da yunkurin kifar da gwamnatinsa da ya tsallake rijiya da baya. Adawa daga al'ummar kasar dai ya sanya dage zaben shugaban kasar zuwa ranar 15, a yayinda a wannan Litinin mai zuwa ne ake saran gudanar da na 'yan majalisa, sai dai har yanzu Burundin na cikin wani wa'adi na tsaka mai wuya.