Buƙatocin Afirka ga taron G20
April 1, 2009Babban saƙon ƙasashen Afrika, wanda Prime Ministan Ƙasar Habasha, Meles Zenawi zai gabatar a wajen Taron ƙasashen da suka fi ƙarfin tattalin arziƙi a Duniya na G20, wanda ake farawa wannan Alhamis dai, shine neman yin la'akari da buƙatun Nahiyar wajen ɗaukacin batutuwan da Taron zai zartar.
Prime Minista Meles Zenawi, wanda ke jagorantar sabon shirin ƙawance raya Afrika, wanda aka fi sani da NEPAD, shine kawai Shugaban Afrikar da Prime Ministan Birtaniya kana mai masaukin baki Gordon Brown ya gayyata, domin halartar Taron, baya ga Shugaban ƙasar Afrika Ta Kudu Kgalema Motlante.
Kimanin makonni biyun da suka gabata dai Mr Zenawi ya je birnin London, domin ganawa da manyan Jami'ai daga Afrika da kuma shi kansa Prime Ministan Birtaniya, a matsayin wani bangare na shirye shiryen Babban Taron duba matsalolin koma bayan Tattalin arzikin da Duniya ke fama dashi.
Sai dai wasu na da ra'ayin cewar ƙasashen da suka ci gaba , ba zasu mayar da hankali sosai ga buƙatun Nahiyar ba, tun da suma tattalin arzikin su na cikin mawuyacin hali, amma a ra'ayin Dakta Aniebo Robert, Babban Jami'i a shirin ƙawancen bunƙasa Duniya, wanda wani reshe ne a sabon shirin ƙawancen raya Afrika NEPAD cewa yayi da sake ga wannan tunanin:
Ba za'a iya keɓe tattalin arzikin wannan ƙasa da ga na wancan ba, harka ce ta cuɗanni in cuɗeka. Matsalar da suke fuskanta zata yadu zuwa gare mu cikin ɗan ƙaramin lokaci, saboda haka, kamata yayi a hada hannu da hannaye wajen shawo kan matsalar, muddin suna son samun ci gaba a wannan karon.
Gabannin wannan lokacin dai, Ministocin kula da harkokin Kasuwanci a Kasashen Afrika, sun gudanar da Taro a Hedikwatar Kungiyar dake birnin Addis Ababa na Kasar Habasha ranar Goma sha Tara ga watan Maris dinnan daya kare. Bayan sun kwashe tsawon jkwanaki biyu suna ganawa, Ministocin sun fitar da mtsayi na bai daya, inda suka bukaci Shugabannin G20, dasu tabbatar da cewa Afrika ta sami wakilci a daukacin batutuwan da suka shafi matsalar koma bayan tattalin arzikin.
To, sai dai Dakta Robert yace idan ma sun cimma wata matsaya, to kuwa yana da ja:
Yace muna bukatar sanin abubuwan dake cikin wannan matsayar, domin a baya an sami wasu Kwamitoci da hukumomi da nufin bunƙasa Afrika, kamar na Blair da sauran su, amma basu tsinana komai ba. Babu wani abin a zo a ganin da Afrika zata yi fatan samu, musamman idan aka yi la'akari da yanayin da aka kira Taron cikin gaggawa.
To, a yayin da ake fuskantar wannan matsalar, wani rahoton da hukumar kula da harkokin tattalin arziki na Majalisar Dinkin Duniya, mai kula da Afrika, ya nunar da cewar Tattalin arzikin Nahiyar zai sami koma baya da kashi Hudu da digo daya cikin dari a wannan shekarar, bayan da yayi ƙasa da kashi biyar cikin dari a bara.
Rahoton ya ,kuma yi kashedin cewar harkar cinikayyar data rauni sosai tsakanin Afrika da Turai da kuma Amurka, game ƙarancin ɗanyen kayayyakin da ake safarar su zuwa ƙasar Sin, da wasu sassa ns Dubiya, matsalar zata janyo koma baya ga ƙasashe dama a Nahiyar.
Asusun bayar da Lamuni a Duniya na IMF, ya fi nuna damuwa, inda yace akwai ,ma yiwuwar bunƙasar ta gaza rabin na bara.
To, ko da shike a makonni biyun da suka gabata, Mr Gordon Brown ya shaidawa shugabannin Afrika cewar zai yaƙi matakin bada kariyar da wasu ƙasashe ke yi, amma akwai buƙatar a zura ido a gani ko zai shawo kan Shugabannin na G20 su dauki wannan mtsayin.
A shekara ta ´dubu ɗaya da ɗari tara da Casa'in da tara ne dai, ƙungiyar ƙasashen dake da ƙarfin tattalin arziƙi na G20 tayi taron ta na fako. Wadannan ƙasashen kuma sune ke wakiltar kashi Casa'in cikin ɗari na kuɗaɗen shiga a Duniya, kana da kashi tamanin cikin ɗari na harkar cinikayya a duniya baki ɗaya.
Mawallafi: saleh Umar saleh
Edita: Yahouza Sadissou Madobi