Bundesliga: Cinikin 'yan wasa mafi tsada a tarihi
Sayan dan wasa Timo Werner daga RB Leipzig zuwa Chelsea ya kasance dan kwallon kafar kasar Jamus mafi tsada a tarihin gasar Bundesliga. Ga wasu daga cikin cinikin 'yan wasa da suka ja hankula.
Ousmane Dembele
Yarjejeniyar cinikin dan wasan daga Borussia Dortmund zuwa Barcelona ta kasance mafi tsada da aka gani a cinikayyar 'yan wasa na duk wata kungiyar kwallon Bundesliga. An biya Dortmund Euro miliyan 105 baya ga kudaden talla, kafin ta amince ta mika shi. Nasara ce babba ga dan shekaru 20 da haihuwan, sai dai har yanzu Dembele bai taka rawar gani tun bayan komawarsa Spain ba.
Lucas Hernandez
Kungiyar Bayern Munich ta kara azama a sayan dan wasa Lucas Hernandez a farkon shekarar 2019, inda ta zuba zunzurutun kudade na Euro miliyan 80 don siyo mai tsaron bayan daga kungiyarsa ta Atletico Madrid, wannan ya sa ya kasance dan wasa mafi tsada a kungiyoyin gasar Bundesliga.
Kevin De Bruyne
Kakar wasan Bundesliga ta shekarar 2015/2016 ta soma da cinikin dan wasa mai armashi. Dan wasan mai cike da basira ya bar kungiyar Wolfsburg inda ya koma Manchester City kan kudi Euro miliyan 74. Babu wata kungiya a Jamus da ta taba samun irin wannan kudin a cinikin dan wasa a wancan lokacin. Yanzu De Bruyne ya kasance daya daga cikin fitattun 'yan wasa na gasar Premier.
Naby Keita
Kungiyar RB Leipzig ta siyo Keita a kan kudi Euro miliyan 15 daga Salzburg. Sai dai kash! Bai dade ba a Jamus kafin kungiyar Liverpool ta yi wuf da shi a kan kudi Euro miliyan 70. Ba karamar riba ba ce ga Keita.
Timo Werner
Gwanin zura kwallo a raga na Jamus ya kasance wanda masu horas da 'yan wasa ke rige-rige a kai. Bayern Munich da Liverpool sune a sahun gaba a kungiyoyin da ke zawarcinsa, sai dai kafin ka ce kwabo kungiyar Chelsea ta kamalla cinikin dan wasan kan kudi Euro miliyan 53. Hakika ya taka rawar gani a tsohuwar kungiyarsa ta RB Leipzig inda yanzu ya bar wagegen gibi.
Leroy Sane
Jita-jita kan zai koma murza leda a kungiyar Bayern Munich, sai dai a wani yanayi na ba-zata, Sane ya bar kungiyar Schalke na Jamus zuwa Manchester City a Ingila a shekarar 2016. Rahotanni sun nunar da yadda aka biya kimanin Euro miliyan 50 a wannan ciniki.
Granit Xhaka
Dan kasar Switzerland Granit Xhaka ya koma Borussia Mönchengladbach a shekarar 2012, kafin a sayar da shi ga kungiyar Arsenal a kan Euro 45. Ba yabo ba fallasa a rawar da yake ci gaba da takawa a gasar Premier ta Ingila.
Julian Draxler
A bazarar shekarar 2016 ya bar kungiyar Wolfsburg ya koma kungiyar Schalke, amma jim kadan ya yanke shawarar raba gari da kungiyar. Sai a watan Janairu ya sami biyan bukata, ya koma taka leda a kungiyar PSG ta kasar Faransa kan kudi Euro miliyan 40. Ana ganin Wolfsburg ta tafka asara ganin ta siyo dan wasan a kan Euro miliyan 43.
Henrikh Mkhitaryan
Ko mene ne dalilin shugaban kungiyar Borussia Dortmund Hans-Joachim Watzke na zura wa dan wasan idanu? Daga kungiyar Shakhtar Donestsk ya koma Dortmund a kan Euro miliyan 27.5 a shekarar 2013, daga nan aka sayar da dan wasan ga Manchester United a kan Euro miliyan 42 bayan nan ya koma taka leda a Arsenal yanzu an bayar da shi aro ga kungiyar Roma.
Corentin Tolisso
Bayern Munich ta siyo dan wasan tsakiya na Faransa da ke wa kungiyar Lyon wasa, Corentin Tolisso a kan kudi Euro miliyan 41.5 a watan Yunin shekarar 2017. A lokacin shi ne dan wasa mafi tsada da aka taba siyo shi zuwa buga gasar Bundesliga ta Jamus.
Roberto Firmino
A cikin kankanin lokaci dan Brazil Roberto Firmino ya kasance dan wasa a gasar Bundesliga mafi tsada. A shekarar 2015, Liverpool ta biya Hoffenheim Euro miliyan 41 a cinikin dan wasan. Ga dukkan alamu hakar ta cimma ruwa ganin jerin nasarorin da kungiyar ta samu sai a ce Firmino ya ci kudinsa.
Javi Martinez
Bayern Munich ta zuba Euro miliyan 40 don siyan Javi Martinez daga Athletic Bilbao. Bayern ba ta yi nadama ba, don kuwa Martinez ya taimaka wa kungiyar a nasarorin da ta samu a lashe gasar Bundesliga sau da dama.