SiyasaJamus
Bundesliga: Murna ta koma ciki
August 10, 2020Talla
Ministocin lafiya sun amince da a ci gaba da mutunta dokar hana taron jama'a har zuwa karshen watan Oktoban 2020, wannan na nufin ba za a bai wa 'yan kallon wasannin Bundesliga damar shiga filin wasanni kamar yadda aka amince a baya ba a yayin soma kakar wasan bana na daga ranar takwas ga watan Satumban bana.
Ministocin sun yanke shawarar ce a wannan Litinin, ganin yadda alkaluman masu kamuwa da cutar ke karuwa. Jami'an kiwon lafiya a na su bangaren, sun sha shawarta gwamnati kan yin takatsantsan a janye dokokin hana yaduwar cutar, sun nemi a ci gaba da daukar matakai na hana yaduwar cutar, da suka hada da sanya takunkumin rufe fuska da saka tazara a tsakanin jama'a.