APC na cigaba da asarar 'ya'yanta
July 31, 2018Talla
Saraki ya bayyana ficewarsa daga APC din ne a wani sako da ya sanya a shafinsa na Twitter. Hakan kuwa na zuwa ne watanni kalilan gabannin babban zaben kasar wanda shugaban Najeriya Muhamamdu Buhari ke neman wani sabon wa'adin mulki. Sanata Saraki, wanda shi ne mutum na uku da ke da karfin iko a mulkin Najeriyar wani jigo ne a jam'iyyar ta APC. A makon jiya ne dai wasu 'yan majalisar dattawa 16 suka sanar da ficewa daga APC din, yayin da wasu 'yan majalisar wakilai 32 su ma suka yi sallama jam'iyyar.