1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubalen sasanta bangarorin da ke rikici a Côte d'Ivoire

Ibrahim Tounkara MAB/MNA
December 15, 2020

Bayan shan rantsuwar yin sabon wa'adin mulki, Shugaba Alassane Ouattara zai fuskanci kalubalen sasanta bangarorin da ke rikici da juna da samar da wanda zai gaje shi idan ya kammala wa'adin mulki.

https://p.dw.com/p/3mkNk
Daga hagu zuwa dama: Gbagbo, Ouattara da Bedie: Shin za a sasanta kuwa?
Daga hagu zuwa dama: Gbagbo, Ouattara da Bedie: Shin za a sasanta kuwa?

A Côte d'Ivoire, kwana guda bayan rantsar da Alassane Ouattara don gudanar da sabon wa'adin mulki, 'yan adawar kasar da dama na ci gaba da kasancewa a kurkuku ko kuma suna gudun hijira. Amma manyan kalubalen da zai fuskanta sun hada da sasanta bangarorin da ke rikici da juna, tare da samar da wanda zai gaje shi idan ya kammala wa'adinsa na mulki.

A jawabin da ya gabatar yayin rantsuwar kama aiki, Shugaba Alassane Ouattara ya yi alkawarin sasanta 'yan kasar domin su zama tsintsiya madaurinki daya. Wannan mataki na zama babban kalubale ga shugaban, kasancewa shekaru 10 bayan hawansa kan kujerar mulki, ya yi tazarce.  Sai dai ya sanar da kirkirar ma'aikata ta musamman da za ta kula da wannan aiki. Karin bayani: Zaben Cote d'Ivoire ya bar baya da kura

"Domin kara karfafa hadin kan kasa, ina shirin kirkiro wata ma'aikatar da ke da alhakin sasanta 'yan kasa cikin kwanaki masu zuwa. Na umarci Firayiminista da ya sake tattaunawa da jam'iyyun siyasa gabanin gudanar da zaben 'yan majalisu."

'Yan adawa irin su Pascal Affi N'Guessam sun kauracewa zaben 15 ga watan Oktoba
'Yan adawa irin su Pascal Affi N'Guessam sun kauracewa zaben 15 ga watan OktobaHoto: Sia Kambou/AFP/Getty Images

Sai dai 'yan adawa a Côte d'ivoire suka ce kafa wannan ma'aikatar ba za ta wadatar ba. Ko da Olivier Akoto, dan majalisa da aka zaba karkashin jam'iyyar PDCI mai adawa ya ce akwai bukatar zama kan teburi guda don sasantawa.

“Kawunan jama'a sun rabu, jam'iyyar PDCI, ta bakin shugabanta, ta yi kira da a shirya zaman tattaunawar kasa. Dole ne Shugaba Ouattara ya saurari masu adawa da shi. Za a iya kirkirar ma'aikatar sulhu, amma idan wadanda ke riciki da juna ba su ba da hadin kai ba, shin wannan ma'aikatar za ta yi karko?"

Karin bayani: Faransa na son Côte d'Ivoire ta rungumi 'yan adawa

Su ma kungiyoyi masu zaman kansu da manazarta al'amuran yau da kullum sun bayyana bukatar samar da tsari na zahiri idan ana son raba Côte d'Ivoire da rikice-rikicen da take fama da su. Geoffroy Kouao na daya daga cikin masu wannan ra'ayin.

"An bayyana niyya a siyasance na sasantawa a karkashin cibiyoyi da dama, wadanda suka samar da matakai da ba a aiwatar da su ba. Amma, mafi muhimmanci shi ne abubuwa na zahiri: misali sakin fursunonin siyasa da sojojin da aka daure a rikicin shekara ta 2010 da kuma kusoshin adawa wadanda aka daure a kwanan nan da kuma dawowar wadanda ke gudun hijira."

Mamadou Touré, mukaddashin kakakin jam'iyyar da ke mulki ta RHDP
Mamadou Touré, mukaddashin kakakin jam'iyyar da ke mulki ta RHDPHoto: Facebook/Mamadou Touré

Sai dai batun neman magaji na ci gaba da zame wa Alassane Ouattara karfen kafa, duba da cewa ya nemi yin tazarce ne bayan rasuwar wanda jam'iyyarsa ta RHDP ta tsayar takara. An ya zai iya samun mutumin da aka yarda da shi, idan aka zo batun mika mulki? Geoffroy Kouao mai nazazin lamuran siyasa ya amsa wannan tambayar yana mai cewa.

"Ban ga yadda kusoshin bangaren zartarwa za su iya tado da maganar maye gurbi ba muddin Shugaba Ouattara na raye. Akwai sunayen da ake ambatowa kamar Ahmed Ouattara, da Adama Bictogo. Amma, ban yi tsammanin cewa na zama wata damuwa a jam'iyyar RHDP ba."

Masharhanta sun yi intifakin cewa babu shakka wannan wa'adi na uku zai kasance mafi sarkakiya ga shugaban na Côte d' Ivoire Alassane Ouattara, saboda 'yan adawa na ci gaba da kalubalantar halaccin wannan wa'adin na uku na mulki.