1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kira domin tsagaita wuta a Yemen

Lateefa Mustapha Ja'afarApril 19, 2015

Jam'iyyar tsohon shugaban kasar Yemen Ali Abdullah Saleh ta yi maraba da batun tsagaita wuta a kasar da Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci ayi.

https://p.dw.com/p/1FAqg
Saudiya na ci gaba da barin bama-bamai a birnin Taiz na kasar Yemen
Saudiya na ci gaba da barin bama-bamai a birnin Taiz na kasar YemenHoto: Reuters/Stringer

Jam'iyyar ta Saleh ta kuma bukaci duka bangarorin da ke cikin rikicin, ciki kuwa har da kasar Saudiya da su yi kokarin ganin batun tsagaita wutar ya tabbata. A wata sanarwa da aka buga a shafin Internet na jam'iyyar General People's Congress GPC ta Ali Abdullah Saleh ta ce za ta yi kokarin ganin an tabbatar da tsagaita wutar. Su dai magoya bayan tsohon shugaba Saleh na taimakawa 'yan tawayen Huthi da suka kwace iko da wasu manyan birnen kasar ta Yemen. Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa daruruwan mutane ne suka hallaka yayin da wasu dubbai suka kauracewa gidajensu tun bayan da Saudiya ta fara jagorantar kai hare-hare ta sama a ranar 26 ga watan Maris din da ya gabata a kan 'yan tawayen na Huthi.