Bukatar tattaunawa da Boko Haram
May 21, 2014Garin Kaduna a Najeriya, ya zama wani dandali na tattaunawa tsakanin addinai. A jihar, Kiristoci da Musulmi daidai wa daida yawansu yake. A duk lokacin da wani sabani ya tashi tsakaninsu, addinan biyu sukan kaiwa junansu hare-hare, to amma a wani yunkuri na kyautata zamantakewa, wasu mutane biyu da suka taba kasancewa abokan gaban juna, wato limamin kirista Pastor James Wuye da Imam Muhammad Ashafa sun kai ga fahimtar gaskiyar cewar,, wajibi ne su kawar da gaban dake tsakaninsu, su kuma hada kai domin aiki tare ga neman zaman lafiya. Saboda wannan kokari nasu ne a shekara ta 2013, gaba daya aka basu lambar zaman lafiya ta Jamus da aka ware sabod nahiyar Afirka.
Wadanan mutane biyu sun gane cewar shawarwari ne suka fi dacewa ga shawo kan duk wani rikici idan ya tashi. Mutanen biyu sun kuma maimaita bukatar tattaunawa dangane da kungiyar Boko Haram. Imam Muhammad Ashafa ya nunar da cewa shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya gabatar da bukatunsa a ili, kuma an sansu. Wadannan bukatu suna iya zama tushen duk wasu shawarwari na neman sulhu.
"Daga cikin wadannan bukatu kuwa, har da neman hukunta wadanda suka yi sanadiyyar kashe wanda ya kafa kungiyar, wato Mohammed Yusuf, wanda ya mutu a shekara ta 2009, bayan da yan sanda suka kama shi. Bugu da kari kuma, kungiyar ta nemi a biya diyya ga iyalan mayakanta da aka kashe."
Haka nan kuma, a wani Video da kungiyar Boko Haram ta fitar a tsakiyar watan Aprilu dake nuna wasu daga cikin 'yan matan da aka sace a garin Chibok, kungiyar Boko Haram ta baiyana sha'awar tattaunawa a game da yiwuwar musayarsu da mayakanta dake tsare.
Ashafa da Wuye duka sun yi korafin cewar gwamnati ya zuwa yanzu bata nuna wata alama cewar da gaske take yi a batun tattaunawa da Boko haram ba. Dangane da haka, Pastor James Wuye yace:
"Akwai yan Najeiya da duka bangarorin biyu suke iya daukarsu amatsayin wadanda basu da hannu a wannan rikkici, wadanda kuma ake iya sanya su su jagoranci tattaunawar."
Kiran tattaunawa da yan kungiyar Boko Haram, yana kuma samuwa ne bisa tsoron cewar halin da ake ciki tsakanin Kiriostoci da musulmi yana iya kara tabarbarewa. Harin baya-bayan nan a yankunan Kiristoci a Kano da kuma tashin hankalin dake karuwa tsakanin Kiristoci da Musumi a garin Jos, duka sun zama alamun dake nuna cewar yan tarzoman na Boko Haram burinsu shine su hada addinan biyu fada da juna.
Ya zuwa yanzu dai basu kai ga samun nasarar haka ba tukuna, amma Pastor Johanna Buro, wanda shima yake cikin masu daidaita zamantakewa tsakanin addinan biyu yace tsoro da rashin yarda da juna yana karuwa.
"Musulmi yana zargin dan uwansa Kirista cewar abin dake gudana a arewacin Najeriya, wani hadin baki ne tsakanin Kirista da Yahudawa na kaskantar da wannan yanki, da al'ummar Hausawa da Fulani suka mamaye shi, yayin da Kirista yake zargin dan uwansa Musulmi da laifin neman fatattakar Kiristoci gaba daya daga yankin na arewacin Najeriya."
A daya hannun kuma, manyan kungiyoyin Musulmi d na kiristoci dake da mazauninsu a Kaduna, basa komai sai zargin junansu. Shugaban kungiyar Kiristoci ta CAN, ko da shike bai fito fili ya fadi haka ba, amma yayi imanin cewar kungiyar Boko Haram, wani shiri ne na koran Kiristocin daga arewacin Najeriya. A daya hannun, Bayero Abdallah, dan majalisar kololuwa ta addinin Musulunci a Najeriya yace yan siyasa su suke da alhakin maida rikicin da kasar take ciki ya zama na addini. Pastor James Wuye saboda haka ne ya yi kira ga shugabannin addinan kasar su rika sassauci a jawaban su.
Mawallafa: Thomas Mösch/Umaru Aliyu
Edita: Usman Shehu