Bukatar karin haske kan batan Khashoggi
October 14, 2018Talla
A wata sanarwa ta hadin gwiwa da suka fidda a wannan Lahadin, kasashen uku suka ce ya zama dole a bayyana wanda ke da hannu wajen bacewar Khashoggi tare da daukar matakai na ladabtarwa.
Kasashen suka ce duniya ba za ta zuba idanu ta kallo ana yi wa 'yan jarida da 'yancin na fadin albarkacin baki karen-tsaye ba, wannan ne ma ya sanya suka ce suna goyon bayan gudanar da binciken hadin gwiwa da Saudiyya da Turkiyya din ke yi kan bacewar dan jaridar.
Turkiyya dai ta ce ta na zaton an kashe Jamal Khashoggi ne bayan da ya shiga ofishin jakadancin kasar tasa, zargin da Saudiyya din ta musanta.