Habasha: Yankin Tigray na fama da yunwa
July 29, 2021Rahotanni sun nunar da cewa, an toshe hanya daya tilo da ake bi wajen kai agaji yankin, biyo bayan harin da aka kaiwa ayarin motocin jami'an Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya a makon da ya gabata. Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA ta bayyana cewa, a yanzu haka akwai manyan motoci makare da kayan abinci 150 da ke jibge suna jiran umurnin jami'ana tsaro a Semera, yayin da wasu 44 suka kama hanyar zuwa yankin na Tigray a ranar Larabar da ta gabata.
Birnin na Semera na zaman fadar gwamnatin yankin Afar da ke kan iyakar gabashin yankin Tigray, a yanzu ya zama hanyar kai kayan agaji tun bayan da aka karya gadoji biyun da ke kan hanyar da ake amfani da ita a baya wajen kai agajin, a karshen watan Yunin da ya gabata. Tun a ranar 12 ga watan Yunin da ya gabatan dai, rabon da kayan agaji su isa yankin na Tigray. Kiyasi ya nunar da cewa abincin da al'ummar da suke bukatar taimako a yankin ke da shi, ba zai wuce wannan Jumma'a ba tare da ya kare ba.