1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar hanzarta sakin Zakzaky a Najeriya

Uwais Abubakar Idris
December 14, 2016

Kungiyar kare hakin jama’a ta Human Rights Watch ta fitar da rahoto ta na kira ga gwamnatin Najeriya ta hanzarta sakin shugaban kungiyar 'yan Shi'a Ibrahim Zakzaky da ma kawo karshen zargin murkushe ‘yan Shi’a a kasar.

https://p.dw.com/p/2UGAb
Nigeria Demo für die Freilassung von Ibraheem Zakzaky
Hoto: picture alliance/AP Photo/M. Giginyu

Kungiyar ta Human Rights Watch da ta gudanar da bincike mai zurfi a kan daukacin al'amarin na ‘yan Shia tun daga faruwar rikicin a ranakun 12 zuwa 14 ga watan Disambar bara, zuwa ga kashe-kashen da suka biyo baya da ma umarnin da kotu ta bayar na a saki shugaban ‘yan Shi'a Ibrahim Zakzaky duka batutuwa ne da ta bukaci a hanzarta kawo karshensa tare da hukunta wadanda aka samu da laifi a kashe-kashen da aka yi.

Human Rights Watch na mai cewa ci gaba da matsin lamba da ma zargi na kashe 'ya'yan kungiyar a jihohin Kaduna da Katsina da Kebbi da Plateau da Sokoto lamura ne da ke bukatar kafa kwamitin bincike mai zaman kansa don tabbatar da adalci ga kowa. Mausi Segun ita ce jami'ar Kungiyar Human Rights Watch a Najeriya ta bayyana wadannan abubuwan da su ke tsoro da ya sanya bukatar gwamnati daukar mataki.

Nigeria Demo für die Freilassung von Ibraheem Zakzaky
Duk sanda mata da yara suka fita muzaharar 'yan Shi'a a na rasa rayuka a NajeriyarHoto: picture alliance/AP Photo/M. Giginyu

"Muna nuna damuwa ne cewa shekara guda bayan arangamar da ta faru a Zariya a 2015 matakin da ake dauka na gefe guda ne kawai na murkushe 'yan shia, abin da ya kara ta'azzara lamarin ma shi ne haramta kungiyar da cewa ta ‘yan ta'adda ce".

Tuni dai kungiyoyi masu zaman kansu ke nuna ‘yar yatsa ga gwamnatin Najeriyar musamman ma dai ta jihar Kaduna a kan yadda ta ke daukan wannan lamari, musamman haramta kungiyar da ma shellar cewa kungiyar na mai aikata ta'adanci a cikin kasa, yayin da ta ke neman kotu ta aiwatar da hukuncin kisa ga ‘yan Shi'a 50.

Nigeria Massaker in Zaria
Makarantu da gidajen wasu 'yan Shi'a sun zama kangwayeHoto: DW/K. Gänsler

Rundinar ‘yan sandan Najeriya dai ta bayyana cewa ta afka wa ‘yan Shi'a ne a arangamar baya-bayan nan da ta faru a Kano lokacin da suka yi kokari tattaki saboda an same su da makamai. Amma ga gwamnatin jihar Kaduna na mai bayyana cewa akwai bukatar fahimtar abubuwan da suka faru domin ba ta da hannu a hare-haren da aka kai wa ‘yan Shi'a . 

A lokutan baya dai gwamnatin Najeriya na mai al'kawarin gudanar da bincike, a irin wadannan rahotani da har zuwa yanzu ba'a kai ga ganin hakan ba, za'a sa ido a ga ko gwamnatin za ta yi aiki da umurnin kotu na sakin Sheikh Zakzaky sanin cewa ta na da wa'adi har zuwa 16 ga watan Janairun shekara mai zuwa.