Habasha: Rikici na kara rincabewa
November 4, 2021Tuni dai shi ma shugaban makawabciyar kasar ta Habasha Kenya, ya yi kiran da a gaggauta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta. Cikin wata sanarwa da ya bayar, Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya ya bayyana rashin tattaunawa a matsayin wani babban abin damuwa. Wannan dai na zuwa ne, a daidai lokacin da ake cika shekara guda da fara rikicin na Habasha da ya lakume dimbin rayuka tare da tagayyara rayuwar mutane da dama da a yanzu haka ke fama da bala'in yunwa. Tun dai a watan Nuwambar shekarar da ta gabata ta 2020 ne, rikici ya barke tsakanin dakarun gwamnati da na mayakan yankin Tigray da a yanzu haka suka kwace wasu muhimman wurare kana suke barazanar shiga Addis Ababa babban birnin kasar. Mayakan na Tigray dai sun samu goyon bayan wata kungiya ta masu dauke da makamai a kasar da ke zaman ta biyu mafi girma a nahiyar Afirka, abin da ya tilasta mahukuntan Habashan sanya dokar ta baci a fadin kasar baki daya.