Buhari: Za a gudanar da sahihin zabe a Najeriya
September 21, 2022Shugaba Muhammadu Buhari ya soma ne da sukar shugabanni kasashen da ke son dauwama kan mulki koda hakan ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar, ya baiyana takaici kan yadda yunkurin yin tazarce ya haifar da tashe-tashen hankula a kasashe da dama.
Daga bisani shugaban da ya dare mulkin Najeriya a shekarar 2015, ya yi alkawarin ganin an gudanar da zabe lami lafiya, sannan ya mika mulki cikin ruwan sanyi, don dabbaka mulkin dimokradiyya a zaben kasar na 2023.
A dai shekara mai zuwa ce Najeriyar, kasar da ta fi kowacce kasa a nahiyar Afirka yawan al'umma, za ta gudanar da babban zabenta inda fafatawar neman kujerar shugaban kasar, ta fi zafi a tsakanin Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC mai mulki da kuma abokin hamayyarsa Atiku Abubakar na jam'iyyar adawa ta PDP