Buhari ya lashe zaben Najeriya
February 28, 2019Talla
A Najeriya, dan takarar jam'iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar, ya ce zai shigar da kara gaban kotu don kalubalantar sakamakon zaben da ya bai wa Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC nasara a babban zaben kasar da aka gudanar a makon jiya. Atikun dai ya fadi hakan ne a wani taron manema labarai da ya kira. A daya bangaren kuwa, Shugaba Buhari, a yayin jawabinsa na farko bayan lashe zaben, ya godewa dinbin al'ummar kasar da suka zabeshi da kuma amanar da suka ba shi kan ya ci gaba da jagorantarsu.