Buhari ya taka matakalar farko ta takara
September 11, 2018Tun da farkon fari shugaban ya ce ba shi da Naira Miliyan 45 da jam'iyyarsa ta saka a matsayin kudin neman fom na takara ta shugaban kasar mai tasiri. Shi Muhammadu Buhari na bukatar albashin shekara da shekaru kafin ya iya kaiwa ga sayen fom din da ke zaman kofar farko ta takara a karkashin jam'iyyar APC.
Sai dai wata kungiyar da ta kunshi 'yan boko da masu kasuwa sun yi karo-karo da nufin biyan bukatar shugaban kasar tare da mika masa fom din da kungiyar ta NCAN ta ce ta yi ne domin Allah kuma ba ta bukatar sakayya. Injiniya Magaji Da'u Aliyu da ke zaman daya daga cikin shugabannin kungiyar ya ce sun share watanni bakwai suna karo-karon da nufin kai wa ga biyan bukatar ta Buhari.
Daga dukkan alamu kyautar fom din dai a tunanin Buhari na zaman alamun sauyin salo da ma kila kai karshen takarar kudi. Shi dai Buhari ya dauki damar tare da godiya ga matasan da a fadar Sakataren gwamnatin kasar Boss Mustapha ke nuna alamu na farin jini na shugaban kasar tsakanin matasan Najeriya.
Abin jira a gani na zaman yadda take shirin kayawa a tsakanin masu takarar da kusan kowa ke bugun kirji, da kuma matasan da ke sama da kaso 60 cikin 100 na 'yan kasar, amma kuma ke zaman na kan gaba ga batun rashin aikin yi.