Buhari ya caccaki Jonathan kan tsaro
February 26, 2015Dan takarar jam'iyyar adawa a zaben shugabacin Najeriya na watan gobe Janar Muhammudu Buhari ya lashi takobin ganin babu wani bangare na Najeriya da zai kasance ba a karkashin ikon gwamnati in har suka kai ga kafa gwamnati.
A wani jawabi da ya yi a cibiyar nan ta Chatham House da ke Birtaniya, Janar Buhari ya ce gwamnatin da zai kafa in ya lashe zabe za ta yi gyara dangane da yadda sojin kasar ke tafi da aikinsu wanda ya ce gwamnatin yanzu ba ta yin abinda ya kamata wajen tafiyar da rundunar sojin kasar da ma yakin da ake da 'yan kungiyar nan ta Boko Haram.
Kan batun na Boko Haram dai, Janar Buhari ya ce ko kusa ba zai amince da yi musu yafiya ba domin kuwa sun aikata laifukun da ya kyautu a ce sun gurfana gaban kuliya don yi musu shari'a dubu da yadda rikicin da suka haifar ya yi sanadin rasuwar mutane kimanin dubu 13.