Bolsonaro ya lashe zaben Brazil
October 29, 2018A kasar Brazil dan takarar jam'iyyar masu tsattauran ra'ayi da kyamar baki Jair Bolsonaro ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a Lahadi bayan da ya samu kaso 55,13 daga cikin dari a yayin da abokin hamayyarsa Fernando Haddad ya samu kaso 44,87 daga cikin dari na kuri'un da aka kada.
Dubban magoya bayan Bolsonaron sun shafe tsawon dare suna gudanar da shagulgulan murna da wasan wuta a biranen kasar da dama. A jawabinsa na farko a matsayin zababben shugaban kasa Jair Bolsonaro wanda ya goyi bayan mulkin kama da sojojin kasar suka yi daga shekara ta 1964 zuwa 1985 ya bayyana cewa Brazil ba za ta ci gaba da tafiya a kan tafarkin kwamunisanci da akidar gurguzu ba.
Kazalika ya sha alwashin kare tafarkin dimukuradiyya da kundin tsarin mulkin kasar da 'yancin fadin albarkacin baki. Ya zuwa yanzu dai abokin hamayyarsa Fernado Haddad bai kai ga yi masa barka da amsa shan kayi ba, amma daga nasa bangaren shugaban kasar ta Barazil mai barin gado Michel Temer tuni ya yi wa sabon shugaban barka.