Brazil ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku
November 29, 2016Kasar Brazil ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku a duk fadin kasar domin nuna alhini ga mutuwar 'yan kasar 75 da suka hada da tawagar 'yan wasan Kungiyar kwallon kafa ta Chapecoense a cikin wani hadarin jirgin sama da ya wakana a yammacin jiya Litinin a kasar kwalambiya.
Mahukuntan kasar ta Kwalambiya sun sanar da yin nasarar ceto mutane shida da ransu, daga ciki har da Helio Hermito Zampier Neto daya daga cikin 'yan kwallon kafar kasar da yadarin ya rutsa da su.
Tuni dai manyan 'yan wasan kwallon kafa da Kungiyoyin kwallon kafa na duniya irinsu Real Madrid Manchester united, Atletico Madrid, Barsalona, Torino da AS Roma, da ma hukumar kwallon kafa ta duniya wato Fifa suka soma bayyana alhinisu a game da mutuwar mutanen a cikin wannan hadarin jirgin sama a shafukansu na tweeter.
A yamamcin Litinin din jiya ne dai jirgin saman wanda ya taso daga birnin Sao Paulo dauke da mutane 81 ya rikito a kusa da birnin Medellin na Arewa maso Yammacin kasar Kwalambiya.