1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar gwamnati a Brazil

January 2, 2023

A ranar Lahadi ce aka rantsar da sabuwar gwamnatin Brazil karkashin jagorancin shugaba Luiz Inacio Lula da Silva.

https://p.dw.com/p/4LcyT
shugaba Lula na Brazil a lokacin da yake jawabi bayan shan rantsuwar kama aiki
Hoto: Jacqueline Lisboa/REUTERS

Shugaba Luiz Inacio Lula da Silva ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasar Brazil. A jawabinsa na farko bayan an rantsar da shi, shugaba Lula ya nuna kyawawan fatan da ya ke da su game da sake gina kasar da kuma sauya dokokin gwamnatin da ta gabata ta tsohon Shugaba Jair Bolsonaro.

Shugaban ya kuma sha alwashin daukar matakin hukunci kan wadanda suka taka dokokin kasar kana ya ce, gwamnatinsa za ta tabbatar da doka. Sai dai ya kara da cewa, hakan baya nufin ramuwar gayya bane ga wadanda suka gabata. Wannan dai shi ne karo na uku da shugaba Lula zai jagoranci Brazil, bayan lallasa abokin hammayarsa tsohon shugaban kasar Bolsonaro a babban zaben kasar da aka gudanar a watan Octoban bara.