Lula zai yaki cin hanci da rashawa a Brazil
August 26, 2022Talla
Lula ya ce zai kawo sabbin tsare-tsare na binciken cin hanci da rashawa da hukunta duk wanda aka kama da laifin idan ya lashe zaben shugaban kasa da za a gudanar a watan Oktoba.
An dai yanke wa tsohun shugaban kasar wanda ya jagoranci Brazil daga shekarar 2003 zuwa shekarar 2010 hukuncin ne kan laifin cin hanci mafi girma a kasar wanda ya haifar wa gomman 'yan siyasa da 'yan kasuwa fuskantar hukunci, sai dai kuma an wanke shi daga baya wanda hakan ya ba shi damar sake neman tsayawa takara.
Kuri'ar jin ra'ayoyin jama'a dai na nuni da cewa, Lula na kan gaba akan abokin hamaiyarsa shugaba mai ci Jair Bolsonaro.