Brazil: Fursunoni sun karbe iko da gidan yari
February 19, 2018Talla
Fursunonin sun karbe iko da gidan yarin tare da yin garkuwa da wasu ma'aikatan da ke tsare gidan kason. Gidan yarin dai shi ne mafi yawan jama'a sama da mutane 2,000 a maimakon mutane 900.
'Yan sanda sun yi gamin gambiza sun kewaye gidan yarin don tabbatar da doka, sai dai kungiyoyi sun dade da kokawa kan rashin kula da ba da abinci da yawan jama'a a gidajen yarin kasar Brazil, abin da ake gani shi ke haddasa tashe-tashen hankula a yawancin lokuta tsakanin jami'an tsaro da masu zaman kaso.
Zanga-zangar gidan yarin ta biyo bayan matakin shugaban kasar Michel Temmer, na umartan sojoji da karbe ikon lamuran tsaro hada da gidan yarin birnin Rio de Janeiro.