Guinea-Bissau ba za ta mika Bozize ba
May 8, 2024Wata babbar kotu ta musamman da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya a Bangui babban birnin kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar ce dai, ta sanar da sammacin kame Francois Bozize a wani mataki na tuhumar da ake masa kan laifukan cin zarafin dan Adam da masu gadinsa lokacin yana shugaban kasa suka aikata tsakanin shekara ta 2009 zuwa 2013 a kurkukun fararen hula da kuma sansanin bai wa sojoji horo. Mai shekaru 77 a duniya, Bozize ya karbe mulkin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a shekara ta 2003 a wani juyin mulki da ya yi, kafin shi ma a kifar da gwamnatinsa bayan shekaru 10. A yanzu dai Bozize na jagorantar babbar kungiyar tawayen kasar, kuma tun a shekara ta 2023 yake neman mafaka a Guinea-Bissau din da Shugaba Umaro Sissoco Embalo ke muka.