1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cote d'Ivoire: Zanga-zangar adawa da shugaban kasa

Antonio Cascais, AH/MNA
August 17, 2020

Zanga-zangar nuna adawa da matakin da Shugaba Alassane Ouattara ya dauka na sake tsayawa takara karo na uku a zaben Cotre d'Ivoire ta yi kamari.

https://p.dw.com/p/3h5ue
Elfenbeinküste I Ausschreitungen in Abidjan
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Al'amura na ci gaba da tabarbarewa a kasar Cote d'Ivoire biyo bayan zanga-zangar da 'yan adawa suka sake yi a karshen mako domin nuna fushinsu ga aniyar Shugaba Alassane Ouattara na sake tsayawa takara a wa'adi na uku a zaben 31 ga watan Okotoban da ke tafe duk da cewar kundin tsarin mulkin ya haramta masa. Yanzu haka 'yan sanda sun cafke daruruwan jama'a a ciki har da shugabannin kungiyoyin farar hula da na 'yan siyasar da ake zargi da tinzira rikicin.

A cikin unguwanni da yawa na birnin Abidjan da kewaye matasa sun karbi kira da kungiyoyin 'yan adawar suka yi musu wadanda suka fantsama a kan tittunan birnin tare da kone tayoyi da saka shinge ko'ina a kan tittuna domin hana zirga-zirgar motoci tare da kona wasu motocin. An yi fito na fito tsakanin 'yan sanda da masu boren a unguwannin Youpougon da Cocodi da Anono da kuma wasu sassan na kewayen birinin. Wani matashin a Anono ya bayyana matsayinsu game da zanga-zangar.

''Alassane Dramane Ouattara ya yanke shawarar karya dokar tsarin mulkin kasa ta Cote d'Ivore, ya yi alkawarin cewar ba zai tsaya takara ba, amma mun yi mamakin yadda ya sake dawowa a kan maganarsa cewa zai tsaya takara a wa'adi na uku.''

A wani jawabi a farkon watan Agusta Alassane Ouattara ya sanar da aniyar sake tsayawa takara
A wani jawabi a farkon watan Agusta Alassane Ouattara ya sanar da aniyar sake tsayawa takaraHoto: Reuters/Press Service Presidency

A cikin kwanaki uku da aka kwashe ana yin zanga-zangar ta kin amincewar da takarar ta Alassane Ouattara daruruwan mutane suka jikkata kana wasu biyar suka mutu.

'Yan sanda sun cafke mutane kusan dari wadanda ake zargi da tinzira jama'a wajen tayar da fitina, daga cikin wadanda aka kama har da Pulcherie Edith Gbalet jagora ta kungiyoyin farar hula, wacce 'yan sanda da kyallayen rufe fuskoki suka cafke ta a daran Asabar zuwa Lahadi a kan zargin tinzira jama'a domin yin fitina. David Samba na daya daga cikin shugabannin kungiyoyi masu fafutuka wadanda ke yin adawa da takarar Alassane Ouattara.

"Ga labarin da muka samu a Yopougon aka saceta, don mu za mu ce sace ta ne aka yi ba kama ta ba. Wasu mutane da suka rufe fuskokinsu suka tafi da ita, muna yin Allah Wadai da haka. Wannan wata barazana ce ta sare mana gwiwa, amma ko kadan ba mu karaya ba abin takaici ne dai.''

Jami'an kwantar da tarzoma sun rika yin amfani da kulake da barkono tsohuwa wajan tarwatsa masu yin gangamin har daura da birnin Abidjan, inda suka fatattaki jama'ar har cikin gida. Marcelline Kouamé Aya, da ke a Abobo ta ce suna cikin tashin hankali.

''Kuna ganin asara da muka yi a yau muna a waje ba mu ma san inda za mu ba, ban san ma yadda za a ce ba, mun watse, mu abin da muke so zaman lafiya.''

Charles Blé Goudé (hagu) da Laurent Gbagbo sun gurfana gaban kotu a The Hague kan rikicin 2010 zuwa 2011
Charles Blé Goudé (hagu) da Laurent Gbagbo sun gurfana gaban kotu a The Hague kan rikicin 2010 zuwa 2011

Tun lokacin da Alassane Ouattara ya bayyana cewar zai tsaya takara a wa'adi na uku ake rade-raden cewar jam'iyyar FPI za ta tsayer da Laurent Gbagbo wanda kotun kasa da kasa da ke a birnin The Hague ta wanke daga zargin aikata kisan masu zanga-zanga a tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shekara ta 2011 wanda a ciki mutane akalla dubu uku suka mutu.

Kawo yanzu akwai fargabar da ake da shi na sake afkuwar irin wannan tashin hankali tsakanin magoya bayan Alassane Ouattara da Laurent Gbagbo idan har 'yan takarar biyu suka sake gamuwa a zaben.