Boko Haram babban ƙalubale ga Najeriya
June 25, 2012A baya dai ya ciza ya kuma tauna da nufin kawo ƙarshen abun da gwamnatin ta kira ta'addanci irin na 'ya'yan ƙungiyar Boko Haram. Kai har ma an kai ga saka wa'adi na watan Yunin da muke ciki domin adabo da annobar da ta shafi sarki da talakan cikin ƙasar ta Najeriya.
To sai dai kuma daga dukkan alamu dabara tana shirin ƙare wa shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da a karon farko ya fito ya amince da irin girman ƙalubalen dake gabansa a yaƙin.
Burin 'yan ta'adda shi ne durƙusar da gwamnati
Jonathan ɗin da ya share tsawon awoyi har biyu yana amsa tambayoyin 'yan jarida dai ya ce babban burin ƙungiyar na zaman durƙusar da gwamantinsa ko ta halin ƙaƙa. Abun da kuma a cewar shugaban ke zaman ummul aba'isin kai hare hare kan coci coci a sassa daban daban na arewacin tarrayar ta Najeriya.
"In ka kalle ɓulla da girman ƙungiyar ta Boko Haram za ka ga akwai sauyin taku da rawa. Kuma sha'awar duk wani dan ta'adda shine rusa gwamanti, in wata dabara ba ta yi aiki ba sai su sauya wata. Shi yasa muma muke sauyawa muna tunanin ya kamata wasu ma su ɗana domin ganin irin sauyin da za mu samu. Ba wai wanda suke nan basu yi ƙoƙari ba. Za mu ci-gaba da sauya tsarin tsaronmu in kuma ta kama da mutanen dake tafi da shi."
Tuni dai shugaban ya sake miƙa goron gayyata ga 'ya'yan ƙungiyar da a baya gwamnatin ta ce ba ta da niyyar tattauna ta'addancin su akan tebur. Tare kuma da tayin ahuwa ga waɗanda suka amince su ajiye makamansu cikin yaƙin.
Sababbin matakan kuma dake zaman na baya baya a yaƙin da ya kai ga hallaka mutane kusan 1000 a farkon watanni shida na wannan shekara da muke ciki kaɗai.
Matakan kuma da daga dukkan alamu suka gaza burge 'yan ƙasar ta Najeriya da ke yi wa gwamnatin kallon wadda ta kasa fahimtar 'ya'yan ƙungiyar har ya zuwa yanzu.
Dr. Usman Mohammed dai na zaman wani mai sharhi kan harkokin siyasa da ma rigingimun a Najeriya.
Harin bom ya zama ruwan dare a arewacin Najeriya
Rashin sanin da ya ɗara dare duhu ko kuma kau da ido don son ra'ayi dai, duk da sababbin matakan na gwamnati dai ana shirin ƙare watan na Yuni tare da ƙara ta'azzarar boma bomai da ragowar hare haren da ya zuwa yanzu suka koma ruwan dare gama duniyar arewacin ƙasar ta Najeriya.
Abun kuma da a cewar Senator Lawali Shu'aibu dake zaman sakataren jam'iyyar CAN ta 'yan adawar ƙasar ya sanya mantawa da karatun makomar ƙasar zama na 'yan PDP da 'yan garin mu zama wajibi a ɓangaren mahukuntan dake jagorantar harkokin ƙasar ta Najeriya a yanzu haka.
Abun jira a gani dai na zaman makomar rikicin da ma tayin gwamnatin da sau biyu ake batun tattaunawa, sau biyun kuma ana rushewa a cikin tsawon watanni uku.
Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Mohammad Nasiru Awal