1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Blinken ya kawo karshen ziyara a Turai

Suleiman Babayo
September 12, 2024

Sakataren harkokin wajen Amirka na kammala ziyarar kasashen Turai da kasar Poland.

https://p.dw.com/p/4kYM1
 Antony Blinken sakataren harkokin wajen Amurka
Antony Blinken sakataren harkokin wajen AmurkaHoto: Roberto Schmidt/Pool/AP Photo/picture alliance

A wannan Alhamis Sakataren harkokin wajen kasar Amirka, Anthony Blinken ke kasar Poland inda yake kammala ziyarar kwanaki uku na kasashen Turai, kuma yakin da ke faruwa tsakanin Rasha da Ukraine, musamman ko Ukraine za ta iya amfani da makaman kasashen Yammacin Duniya wajen kai hare-haren cikin Rasha ke daukan hankali. Blinken wanda ya isa kasar ta Poland daga Birtaniya, inda ya gana da Sakataren harkokin wajen kasar David Lammy.

Kana ana sa ran gobe Jumma'a Firaminista Keir Starmer na Birtaniya zai kai ziyara fadar mulki ta White House ta Amirka inda zai gana da Shugaba Joe Biden. Kasashen na Birtaniya da Amirka suna sahun gaba wajen taimakon Ukraine tun lokacin da ta fara fuskantar kutse daga dakarun Rasha.