Birtaniya za ta kara tallafar NATO
June 21, 2015Talla
Birtaniya ta bayyana cewa a shirye take ta kara tallafin da ta ke bayarwa ga kungiyar tsaro ta NATO a kokarin samar da tsaro a yankin gabashin Turai ta hanyar kara wa'adin lokacin da dakarunta za su ci gaba da ayyukansu karkashin kungiyar.
Ministan harkokin tsaron Birtaniya Michael Fallon shi ya bayyana haka a ranar Lahadin nan.
Ana dai kara karfin sojin na kawancen NATO a yankin gabashin na Turai tun bayan zargin kasar Rasha da kokarin yin kutse a Ukraine, zargin da mahukuntan na birnin Masko ke karyatawa.
A cewar Ministan harkokin tsaron Birtaniya Fallon, ya zama wajibi a ci gaba da tura wa shugaban kasar ta Rasha Putin sakon cewa kasashen na NATO kansu a hade yake.