Boris Johnson: Murna ta koma ciki kan yarjejeniyar EU
October 19, 2019A yayin wani zama da majalisar dokokin Birtaniya ta yi na musamman wanda shi ne na farko da ta yi a ranar Asabar cikin shekaru 37 da suka gabata, 'yan majalisar sun kada kuri'ar jinkirta bayyana matsayarsu kan batun na fitar Birtaniya daga tarayyar Turai.
Fitaccen dan majalisar nan Oliver Letwin ne ya gabatar da wannan kuduri gaban majaliasar inda ya bukaci da a jinkirta batun ficewar kasar daga EU har sai an warware wasu abubuwa da dama da ya ce suna kunshe da sarkakiya, batun da ya samu karbuwa a wajen 'yan majalisar.
Kakakin majalisar dokokin Birtaniya din John Bercow ya ce sakamakon kuri'ar da aka kada ya nuna cewar 'yan majalisa 322 ne suka amince da kudurin na Letwin yayin da 306 suka kada kuri'ar kin amincewa. Wannan sakamako dai na nufin yanzu dole a sake dage ranar ficewar Birtaniya din daga EU inda tuni ma 'yan majalisar suka bukaci Firaminista Johnson da ya tuntubi EU din don a tsawaita lokacin.
Sai dai Boris Johson ya ce ba zai mika wannan bukata ba ga Kungiyar EU domin ba wata doka da ta tilasta masa yin haka, yana mai cewa "jinkirata fitarmu daga Kungiyar Tarayyar Turai zai kasance abu maras kyau ga kasarmu da EU sannan abu ne maras kyau ga demokradiyya."
A yayin da Firaministan Birtaniya Boris Johnson ke ci gaba da hawa kan wannan matsayi na nuna yin tirjiyar kan tafiya Brussels don neman wani karin wa'adi, a share guda madugun 'yan adawa na kasar Jeremy Corbyn ya ce dole ne shugaban ya bi doka.