Brexit: Birtaniya da EU sun bude sabon babi
April 20, 2020Talla
Taron na zuwa ne bayan makonni goma sha daya da Birtaniya ta balle daga kungiyar kasashen Turai. A yanzu bangarorin biyu na fatan kulla yarjejeniyar kasuwanci a tsakaninsu. Bayan wannan tattaunawar EU da Birtaniya za su sake zama a tsakiyar watan Yuni don ci gaba da kakkabe sauran abubuwan da ka iya tasowa bayan fitar Birtaniya daga EU a watan Janairun da ya gabata.
Kawo yanzu dai Birtaniya tana cikin harkokin kasuwanci na Turai kuma tana cikin kungiyar hukumomin kwastom na nahiyar. Kazalika Birtaniya na ci gaba da bayar da gudunmawarta a kasafin kudi na kungiyar EU din. Sai dai idan har zuwa karshen wannan shekarar basu sake kulla wata sabuwar yarjejeniya ba to kowa zai kama gabanshi.