Bindow: Ba zan goyi bayan Atiku ba
November 29, 2017An yi ta hasashen Atiku Abubakar zai tafi da wasu da dama daga cikin 'yan jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya da ta fada cikin halin rudani musanman bayan da tsohon mataimakin shugaban kasar ya sa kafa ya bar jam'iyyar, sai dai daga dukkan alamu tana shirin rushewa ga Atikun da ke da shirin zama sabon jagora ga bangaren adawa amma ya ke fuskantar turjiyar cikin gida tun daga yanzu.
Kasa da mako guda da ficewa a cikin APC da ya zarga da kasancewa 'yar kama karya, gwamnan jiharsa ta Adamawa Jibrill Bindow ya ce ba shi da shirin goyon baya ko hada inuwa da Atiku da ke neman mafaka a cikin inuwar PDP yanzu, ya ce yana matukar girmama wazirin Adamawar a matsayin dattijon siyasar Najeriya, amma kuma ba zai yi masa biyayya ga bukatar hada kai tare domin gina sabuwar adawa ba
Akasarin gwamnonin jam'iyyar APC mai mulkin sun yanke hukuncin ko Buhari ko kafar katako a kasar da sannu a hankali ke daukar fasali na siyasar gobe. Bindow na zaman kan gaba a cikin karatun na Buhari har Mahdi sakamakon kokarin shugaban wajen tura ta'addanci ya zuwa tarihi. Buhari da ke ziyarar aiki a kasar Ivory Cost ya baiyana niyarsa ta sake tsayawa takarar shugabancin kasar. Abun jira a gani dai na zaman yadda ta ke iya karewa a tsakanin masu karatun maimatawar da masu kallon sai ta sauya cikin kasar da ke kara kusantar zabe.