Binciken mutuwar 'yan cirani
March 16, 2021Majalisar Dinkin Duniya ta nemi a kaddamar da bincike kan musababbin gobarar da ta halaka gomman 'yan cirani a Aden babban birnin kasar Yemen. Matakin majalisar ya biyo bayan zargin da Hukumar Human Rights Watch tayi na cewa mayakan Houthi ne suka haifar da gobarar. Wakilin majalisar a Yemen, Martin Griffiths ya fada ma wani taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa, akwai bukatar daukar mataki don gano wadanda keda hannu a aika-aikan domin a hukuntasu.
A dai ranar bakwai ga wannan watan na Maris ne, wuta ya tashi a wani kebabben wuri da ake tsare da daruruwan 'yan ciranin, rahotanni sun tabbatar da yadda wasu da ake zargi mayakan Houthi ne suka harba abubuwan fashewa da ake zaton sun hadassa gobarar da ta raunata kimanin mutum dari da saba'in, daga bisani an yada wasu hotunan bidiyo da ke nuna konannun gawarwakin watse a cikin dakin ginin. Akasarin wadanda bala'in ya rutsa da su, sun fito ne daga kasar Habasha da ke yankin kahon Afirka.