Bikin Tunawa da yaƙin duniya na biyu
September 11, 2014Shugaban ƙasar Poland na daga cikin manyan baɓin da aka gayyato domin bukukuwan a gaban majalisar dokokin Jamus ta Bundestag. Shugabannin na Jamus da na Poland su dukkaninsu sun yi tuni da irin abubuwan da suka faru a lokacin yaƙin.
Bronislaw Komorowski ya rasa kawunsa a cikin yaƙin duniyar na biyu
Shugaban na Poland Bronislaw Komorowski,wanda mahaifinsa ya yaƙi Jamus a lokacin yaƙin yana tune sossai da irin wahalolin da sojin Jamus suka fuskanta a lokacin yaƙin na duniya. Wanda a ciki Komorowski ya rasa wani wanda ke zaman kawunsa a cikin sansanin gwale-gwale kana aka kori iyayensa daga ƙasar. Shugaban na Poland ya yaba game da fahimta da haɗin kai da Jamus ta bayar a cikin lokacin kaɗan da kuma tuna tarihi domin ƙalubalantar harkokin rayuwa na gaba.
"Dole mu tuna tare kuma da sanin cewa kowa ya ji jiki a yaƙin duniyar na biyu. Ba kwai waɗanda yaƙin ya shafa ba, har ma da 'yan ƙasashen da suka janyo fitinar."
An samu babbar asara a yaƙin da mutane miliyan 62 suka mutu
Yaƙin duniyar na biyu shi ne yaƙi mafi girma da aka yi cikin shekaru shida. Daga shekarun 1939 zuwa 1945 wanda mayaƙa dubu ɗari daga ƙasashen duniya daban-daban har 61 suka fafata wanda a cikinsa. Mutane miliyan 62 suka rasa rayukansu galibi fararar hula. Norbert Lammert shi ne shugaban majalisar dokokin Jamus
"Muna nuna alhini ga mummunan yaƙin da ya auku a cikin tarihi.Yaƙin da Jamus ta haddasa,wanda kuma ya janyo mummunan bala'i ga al'umma."