1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Musulmai sun yi bikin Sallar layya

Suleiman Babayo MAB
June 29, 2023

Musulmai a sassan duniya na ci gaba da bubukuwan Sallar layya. Haka al'umomin kasashen Larabawa sun bi sahun sauran Musulman duniya wajen gudanar da bukukuwan Sallar layya.

https://p.dw.com/p/4TF3R
Indiya | Bikin Sallar layya
Bikin Sallar layya a IndiyaHoto: Subho Singha

A kasar Sudan duk da rikicin da ke wakana Musulman kasar sun yi bikin Sallar layya kamar sauran takwarorinsu na kasashen duniya, yayin da a kasashe irin Najeriya ake fama da tsadar rayuwa.