1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karrama sojojin da suka shiga yakin Afghanistan

Ramatu Garba Baba
October 13, 2021

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta jagoranci taron karrama sojojin kasar da suka shiga yakin Afganistan don fada da mayakan Taliban daga shekarar 2002.

https://p.dw.com/p/41dzX
Russland | Angela Merkel bei Kranzniederlegung in Moskau
Hoto: Alexander Zemlianichenko/AP/picture alliance

Shugabanin Jamus sun gudanar da wani muhinmin taro don karrama sojojin kasar da suka sadaukar da rayukansu a tsawon shekaru ashirin da rundunar sojin kasar ta kwashe a yakin kasar Afghanistan.

Shugabar gwamnati Angela Merkel da Shugaba Frank-Walter Steinmeier da sauran manyan jagororin gwamnati ne suka halarci taron na birnin Berlin a wannan Laraba. Sojojin Jamus kimanin 150, 000 aka tura Afghanistan a farkon shekarar 2002. Jamus ta rasa kimanin sojojinta 59 kafin ta sanar da janye rundunar bayan da Taliban ta kwace mulki a watan Augustan da ya gabata.