1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin al´adun gargajiya a Kaduna

July 24, 2009

Bikin ya samu halarcin dukkan ƙananan hukumomin jihar Kaduna.

https://p.dw.com/p/IwHD
Hoto: picture-alliance/ dpa

Kamar a kowace shekara a bana ma jihar Kaduna dake arewacin tarayyar Najeriya ta gudanar da bikin al´adun gargajiya na Kaduna State Festival of Atrs and Culture wato Kadfest a taƙaice don samar da waɗanda za su wakilci jihar a wasannin al´adun gargajiya na ƙasa baki ɗaya wato NAFEST wanda a bana birnin Minna hedkwatar jihar Neja zai karɓi baƙoncinsa.

Kowace ƙaramar hukuma ta jihar ta Kaduna ta aike da nata ´yan wasannin al´adun gargajiya don shiga gasar fid da gwanin. An dai kwashe kwanaki biyar ana gudanar da wannan biki a Kaduna ƙarƙashin taken muhimmancin al´adunmu da kuma ƙalubalen da suke fuskanta na wannan zamani.