Benjamin Netayanhu ya kare kansa daga zargin cin hanci
January 2, 2017Talla
Netanyahu ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai gabannin ammsa kiran 'yan sanda wadanda za su yi masa tanbayoyi game da zargin:''Na fada muku kuma na nanata babu abin da aka yi kuma babu abin da za a yi.''Ana zargin firaministan na Isra'ila da cewar ya karbi gomai na miliyoyin daloli daga shugabannin kamfaoni da 'yan kwangila.