1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yanto Turawa mayakan jihadi

Ramatu Garba Baba
July 17, 2021

Gwamnatin Beljiyam tayi nasarar 'yanto wasu 'yan kasar da suka shiga yakin Siriya da sunan jihadi. Sun hada da mata da yara masu kananan shekaru.

https://p.dw.com/p/3wcF4
Frankreich Roubaix Schießerei mit Geiselnahme
Hoto: picture-alliance/dpa/H. Van Maele

'Yan kasar goma sha shida aka ceto daga wani gidan yarin da ake tsare da mayakan jihadi a kasar Siriya. Yaran goma masu kananan shekaru da matan shida, dukkansu Turawan Beljiyam ne, amma suka shiga yakin Siriya da sunan jihadi. Jim kadan da isarsu Beljiyam aka mika matan hannu hukuma a yayin da aka kai yaran wata cibiyar gyaran hali a  wannan Asabar

Daruruwan mayakan sa kai daga sassan kasashen Turai, sun shiga yakin kasashen Siriya da Iraki, a lokacin da Kungiyar IS ke yada da'awar jihadi a sassan duniya, rahotanni sun ce, da dama daga cikinsu, sun rasa rayukansu, sai dai kawo yanzu akwai wadanda suka yi raguwa a sansanonin da mayakan IS keda karfin iko. Sannu a hankali wasu daga cikin kasashen Turan na kwaso 'yan kasarsu a yayin da wasu suka zabi raba gari da su.