1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bayanin shugaban bankin Turai kan matakinsa a kan rikicin kudin Euro

October 24, 2012

Shugaban babban bankin Turai, Mario Draghi a gaban majalisar dokokin Jamus ya kare matakan da bankin ke ɗauka wajen tinkarar rikicin kudin Euro.

https://p.dw.com/p/16VvP
Hoto: AP

Yayin wani zama da komitin Tarayyar Turai a kan kasafin kuɗi ya yi Draghi ya amsa tambayoyi daga masu sukan lamirin bankin musamman sanarwar da bankin ya bayar cewa zai gaggauta sayen takardun basukan ƙasashen Turai da ke fuskantar matsala. Yayin ziyarar da ya kai a majalisar dokokin Jamus ta Bundestag domin yin bayani game da halin da ake ciki Draghi ya ce ya zamo wajibi bankin ya ɗauki wannan mataki saboda tsoron yiwuwar faɗuwar darajar kuɗin Euro warwas. Ya ce sayen takardun basukan ba zai kai ga yin rufa- rufa game da tsarin kuɗin ƙasashe ba, ba zai kuma janyo ƙaruwar tsadar rayuwa ba.

Babban bankin Jamus dai bai yi wata-wata ba ya nuna rashin amincewarsa da ɗaukar wannan mataki. Hakazalika Draghi na ci gaba da shan suka daga gwamnatin gamin gambizar CDU da FDP game da matakan da yake ɗauka wajen ceto kuɗin Euro.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal