Magunugnan Jabu a Airka na karuwa
March 8, 2019A babbar kasuwar Ouagadougou ana da wata kasuwar bayan fage inda masu tallan maganin ke fakewa a bayan rumfuna ko kuma su zuba magungunan da suke sayarwa a cikin aljihu. Magungunan na jabu sun hada da Ibuprofen da paracetamol da antibiotics da kuma maganin malaria wato zazzabin cizon sauro da ma dukkan wasu nau'in magunguna.
Hukumar lafiya ta duniya ta kiyasin cewa magungunan jabu sun fi yawa a Najeriya inda ake da kashi 64 cikin dari na magungunan Jabu.
Kiyasi ya nuna yan kasuwar na hada hada ta kai ta dala biliyan 200 daga kayan jabu. Jaridar ta ce wannan matsalar tana ciwa ma'aikatun lafiya da hukumomin tsaro da ma likitoci a fadin duniya tuwo a kwarya. A cewar hukumar lafiya ta duniya WHO kasashen China da Indiya na daga cikin kasashen da suka fi kaurin suna wajen yin magungunan jabu bayan kasashen Paraguay da Pakistan da kuma Birtaniya.
Kayayyaki da dama ne dai aka dauke aka tafi da su Ingila a zamnin mulkin mallaka wanda yanzu ake kokarin dawo da su
Gidan adana kayan tarihi na London zai mayar wa da kasar Habasha sumar wani basaraken kasar na tun zamanin mulkin mallaka. Wannan shi ne taken sharhin da Jaridar Süddeutsche Zeitung ta wallafa. Sumar ta sarki Tewodros na biyu na ajiye ne a gidan kayan tarihi na yaki na Birtaniya fiye da shekaru 150 da suka wuce. Ga 'yan Kasar Habasha dai wannan tamkar sane ne aka yi musu kuma kasar ta bukaci a dawo mata da sumar basaraken nata. A ranar Litinin Birtaniyar ta amince za ta mayar da sumar ga kasar habasha cikin 'yan watanni masu zuwa. Al'ummar Habashar za su kasance cikin alhini da jimami yayin da za su karbi wannan suma ta basaraken nasu na tsawon zamani. A kasashen Turai dai an dade ana muhawara kan mayar wa da Afirka kayan tarihi da aka dauke daga nahiyar. A makon da ya gabata wata tawaga daga Baden-Würtemberg a nan Jamus ta mayar da wani Littafin Bible da kuma tsumagiya na ayan kabilar Heroro a Namibiya. Haka ma dai kasashen Turai da dama suna son mayar wa Najeriya sassake-sassake na tagulla da aka aro daga Benin. Wannan kadan ne daga cikin kayan tarihin Afirka da ke jibge a kasashen Turai. Musamman shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi alkawarin mayar da kayayyaki kimanin dubu 90 na Afirka da ke Faransa. Sai dai lamarin ba haka yake ba a nan Jamus inda wasu shugabannin gidajen tarihi ke cewa wasu daga cikin wadannan kayayyaki na tarihi an samo ne ta hanya ta halali a lokacin mulkin mallaka.