1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya na cikin rudanin rashin tsaro

July 26, 2022

Mahukuntan Najeriya sun yi watsi da barazanar barayin daji da ke fadin suna shirin kaiwa har ga shugaban kasar a nan gaba.

https://p.dw.com/p/4EdCW
Nigeria JSS Sicherheitskräfte in Jangebe
Rundunar kiyaye zaman lafiyaHoto: Afolabi Sotunde/REUTERS

A yayin da ake ci gaba da shiga rudani bisa makomar fasinjojin jirgin kasar Kaduna – Abuja, wani faifen bidiyo da a cikinsa barayin ke dukan kamammun dai ne ya tada hankali a daukacin Najeriya a halin yanzu.

Kuma a Abuja 'yan uwan kamammun dai sun share tsawon wunin wannan rana ta Litinin suna wata zanga zanag a hedikwatar ma'aikatar sufuri ta Najeriya bisa neman kara matsin lambar ceto mutane akalla 43 da ke a hannun barayin.

Sannu a hankali dai ana kallon rikidewa ta bukatar barayin da tun da farkon fari suka ce suna bukatar a sako musu 'yan uwansu, kamun sauyawa zuwa ga neman fansa ta kudade.

Nigeria Polizeikräfte in Lagos
Rundunar 'yandan NajeriyaHoto: Olukayode Jaiyeola/NurPhoto/picture alliance

Hajiya Bilkisu Ahmed dai na cikin masu zanga zangar da ta ce an kama 'yar uwarta da 'yarta mai shekaru guda biyu kuma ke neman gwamnatin kasar ta mika wuya da nufin biyan kudaden fansar da barayin ke nema.

Majiyoyi na tsaro dai sun ce gaza kaiwa ya zuwa biyan wasu Naira Miliyan Dari Uku da 'yan uwan kammamun suka tara ne dai ya kai ga harzuka barayin ya zuwa yin faifen bidiyon da nufin matsa lamba ga Abujar da ke dada fuskantar matsala cikin kasar a halin yanzu.

Jami'an tsaron kasar a makon da ya shude dai sun yi nasarar kame kudaden da aka tsara kaisu ga tunga ta barayin da nufin sakin wasu karin mutum uku cikin kammamun.

Abujar da ta ce ta biya wasu a ciki na bukatu na barayin ta ce akai ga kasuwa batun biyan kudaden fansar a fadar Malam Garba Shehu da ke zaman kakaki na fadar gwamnatin Najeriyar.

Frankreich Paris | Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu BuhariHoto: JULIEN DE ROSA/AFP/Getty Images

Koma ya take shirin kayawa a tsakanin hukumomin da ke fadin ba fansa ga barayin da ke dada fitar da burinsu a fili dai, rikicin dai na dada tasiri a Abuja inda barazana ta aiyukan na ta'adda ke tasiri ga rayuwar al'ummar birnin.

Makarantu na gwamnatin tarayyar dai sun kulle da nufin kaucewa hari na barayin, da ke kara barazana ga rayuwa ta mazauna birnin.

An dai dauki lokaci ana fuskantar karuwar aiyuka na masu ta'addar a garuruwan da ke zagaye da Abujar a wani kokari na kawanya kan birnin da ke zaman mattatarar 'yan mulki na kasar.