Barazanar tsaro na kara kamari a Kaduna
August 3, 2016A cewar mazauna yankin Kudancin Kadunan, sun yi tunanin daukar matakan kare kawunansu ne sakamakon abin da suka kira da gazawar hukumomi wajen karesu da iyalansu. Tsawon shekaru ne dai yankin na Kudancin Kaduna ke fama da ayyukan na 'yan bindiga da ya hadar da satar mutane domin yin garkuwa da su har sai an basu dimbin kudin da suka bukata, a wasu lokutan ma su kan kashe wadanda suka kama din suka kuma yi garkuwa da su.
Mazauna yankin na Kudancin Kaduna sun nunar da cewa an san wadanda ke yawo da bindiga suna kashe mutane, wanda kuma hakan ya tilasta wa mazauna yankin musamman ma manoma fargabar zuwa gonakinsu ta yadda suka ce ana iya fuskantar karancin abinci dangane da wannan dalili, wanda suka ce ya zama tilas su tashi tsaye domin kare kansu daga wannan barazana da suke fuskanta.
Matan yankin na Kudancin Kadunan ma dai ba a barsu a baya ba wajen nuna takaicinsu kan barazanar da suke fuskanta, inda suka gudanar da wata zanga-zanga kan abin da suka ce ana kashe musu 'ya'yansu da mazajensu. Kwamared Nasir Jagaba shi ne shugaban matasan yankin Kudancin na Kaduna ,ya kuma ce ya zama wajibi su hada kan matasa su rinka aikin sintiri da banga a yankunansu domin su kare kansu.
A nata bangaren rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta bakin kakakinta ASP Aliyu Abdullahi Usman cewa ta yi rundunar ba ta barci kuma ta kara tsaurara matakan tsaro. ASP Usman ya kuma bukaci al'umma da su rinka taimaka wa hukumomin tsaro da bayanan sirri domin shawo kan duk wata barazana ta tsaro da jihar ke fuskanta.
Masana dai na alakanta yawaitar ayyaukan 'yan bindiga da ma su garkuwa da mutanen, da yaduwar kananan makamai a tsakanin al'umma, abin da suka bukaci da a yi kokarin kawo karshensa.